3 Janairu 2022 - 16:39
​Burkina Faso: ‘Sojoji 11 Sun Rasa Rayukansu A Wani Harin 'Yan Ta'adda

A Burkina Faso akalla sojojin kasar 11 ne suka rasa rayyukan su,yayinda suka samu nasarar kashe yan ta’adda 29 a wani hari da yan bindiga suka kai ranar asabar a wani kauye dake Gomboro a arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Rahotanni daga hedikwatar tsaron kasar na nuni cewa a wannan barin wuta na ranar Asabar dakarun kasar 11 ne suka kwanta dama.

Babban hafsan sojan kasar Janar Gilbert Ouedrago ya jajantawa iyalan sojojin tare da ziyartar wadanda suka samu raunuka wadada suke kwance a asibitia halin yanzu.

Tun a shekara ta 2015 ne kasar ta Burkina Faso ta fuskanci hare-haren yan ta’adda da suka hadasa asarar rayukan jama’a tare da tilastawa da dama tserewa daga yankunan su.

Mayakan ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi da ke cikin kasar Mali ne suke yin barazana ga zaman lafiyan kasar ta Burkina Faso.

342/